in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawarar "ziri daya da hanya daya" na sanya hadin gwiwar moriyar juna tsakanin kasashen Sin da Masar ta hau kan wani sabon mataki
2017-09-08 10:56:06 cri

A 'yan shekarun nan, kasashen Sin da Masar na fadada hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya da kuma zuba jari bisa shawarar "ziri daya da hanya daya". A lokacin da kamfanonin kasar Sin suke kyautata tsarin turakun tattara wutar lantarki da kogin Suez na kasar Masar, su kansu suna samun bunkasa cikin sauri sabo da 'yan kwadago masu arha da manufofin kasar Masar. Yanzu a lokacin da ake aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", ana kyautata zaton cewa, hadin gwiwar moriyar juna tsakanin kasashen Sin da Masar za ta kai wani sabon mataki.

Tun bayan shekarar 2014, gwamnatin kasar Masar ke kokarin bunkasa zirin tattalin arziki dake dab da kogin Suez, da aikin kyautata tsarin manyan turakun tattara wutar lantarki da kuma tsarin layukan dogo, ta yadda za a iya ciyar da tattalin arzikin kasar gaba. Wadannan Sun kuma zama muhimman ayyuka ga kamfanonin kasar Sin wadanda suke neman ci gaba a kasar Masar.

Mr. Han Bing, wani jami'in dake kula da harkokin tattalin arziki da cinikayya a ofishin jakadan kasar Sin dake kasar Masar ya ce, gwamnatin kasar Masar na mai da hankali sosai kan sakamakon da kasar Sin ta samu wajen samar da kayayyakin more rayuwar jama'a cikin shekaru fiye da 30 da suka wuce. A halin da ake ciki yanzu, kamfanonin kasar Sin dake kasar Masar suna samun kwangilolin dake shafar sufuri da wutar lantarki da sadarwa. Wannan ya shaida cewa, kasar Masar ta yi ammana da sakamakon da kasar Sin ta samu wajen bunkasa tattalin arziki.

Amma yanzu ban da irin wadannan ayyukan da kamfanonin kasar Sin dake kasar Masar suke ci gaba da yi, sun kuma fara mai da hankali kan hadin gwiwar moriyar juna a fannonin samar da makamashi da kuma sha'anin kudi.

Kasar Masar wadda take da isassun kwadago, kuma ta kasance kamar wata babbar kasuwa, ta kasance a wurin dake hade kasashen Afirka da nahiyar Asiya. A 'yan shekarun nan, kasar Sin na aiwatar da manufar hadin gwiwa da kasashen Afirka a fannin samar da makamashi, inda wasu kamfanonin kasar Sin suka yi amfani da wannan manufa wajen samun ci gaba a kasar Masar.

A yankin hadin gwiwar tattalin arziki dake dab da kogin Suez da kasashen Sin da Masar suka kafa tare, reshen kasar Masar na kamfanin JUSHI na kasar Sin zai cimma burinsa na samar da gilashi mai sirkin roba ton dubu dari 2 a shekara guda. Mr. Yang Jixiang, mataimakin babban direktan reshen Masar na kamfanin JUSHI na kasar Sin, ya shaidawa wakilinmu cewa, za a sayar da kayayyakinsu na gilashi mai sirkin roba a kasuwannin Turai da kasashen gabas ta tsakiya da kuma kasar Masar.

Kayayyakin abincin dabbobin gida da reshen kasar Masar na kamfanin New Hope na kasar Sin ke samarwa, ya kai kashi 10 zuwa kashi 15 cikin dari a kasuwar kasar Masar. Bisa shirin da kamfanin ya tsara, a cikin shekaru biyu masu zuwa, zai kaddamar da sabbin masana'antu 3 a kasar Masar. Mr. Yang Chengbin, babban derektan kamfanin New Hope reshen kasar Masar ya bayyana cewa, bayan ya kafa reshensa a kasar Masar a shekarar 2010, kamfanin ya na kokarin neman ci gaba bisa ma'anufofin kasar Masar da fasahohin zamani da yake da su. Sakamakon haka, kayayyakin da kamfanin ke samarwa sun samu karbuwa a kasar.

A lokacin da kamfanonin kasar Sin ke samun ci gaba cikin sauri a Masar, suna kuma mayar da martini ta hanyar taimakawa al'ummomin kasar. a yanzu adadin ma'aikatan kasar Masar ya kai kashi 97 cikin dari na dukkan ma'aikatan da suke aiki a reshen Masar na kamfanin JUSHI a yayin da adadinsu ya kai fiye da kashi 90 cikin dari a rashen Masar na kamfanin New Hope na kasar Sin.

Bisa kididdigar da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta bayar, ya zuwa karshen shekarar 2015, yawan jarin da kamfanonin kasar Sin suka zuba a kasar Masar ya kai dalar Amurka miliyan 663, sannan yawan masana'antun da kamfanonin kasar Sin suka gina a kasar Masar ya kai fiye da 1200 wadanda suke samar da guraben aikin yi fiye da dubu 11.

Har ila yau, kasashen Sin da Masar na yin hadin gwiwa cikin sauri a fannin hada-hadar kudi, Har ma manazartan kasar Masar na kyautata zaton cewa, irin wannan hadin gwiwa za ta kara ingiza hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu.

A shekarar 2009 ne, bankin bunkasa kasar Sin ya kafa ofishinsa a kasar Masar. Kuma kawo yanzu, ya samar da rancen fiye da dalar Amurka biliyan 2 ga kasar Masar ta hanyar yin hadin gwiwa da hukumomin kudi na kasar, ciki har da babban bankinta.

Sannan bankin kula da kayakin shigi da fice da bankin ICBC da kamfanin ba da inshora ga kayayyakin shigi da fice dukkansu na kasar Sin, sun kafa wani tsari domin nuna goyon baya ga kyautata tsarin turakun tattara wutar lantarki na kasar Masar.

Wani mataimakin gwamnan bankin Masar ya ce, shawarar "ziri daya da hanya daya" ta samar da wata kyakkyawar dama ga kasashen Sin da Masar, wajen yin hadin gwiwa a fannin hada-hadar kudi.

Yanzu dai, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannonin tattalin arziki da hada-hadar kudi na samun ci gaba kamar yadda ake fata. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China