in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kafa kawancen wuraren adana kayayyakin tarihi na kasashen dake kan hanyar siliki
2017-05-19 10:49:56 cri

Jiya Alhamis 18 ga wata, rana ce ta wuraren adana kayayyakin tarihi ta duniya, a bana an shirya bikin tunawa da ranar a nan birnin Beijing, domin taya murnar ranar, a nan birnin Beijing wuraren adana kayayyakin tarihin da yawansu ya kai 97 sun bude kofa ga jama'a ba tare da karbar kudi ba. A yayin bikin da aka shirya a babban dakin adana kayayyakin tarihi na birnin Beijing, shugaban hukumar kula da aikin kare kayayyakin tarihi ta kasar Sin Liu Yuzhu, ya bayyana cewa ya zuwa shekarar 2016, adadin wuraren adana kayayyakin tarihin da aka yi rajistar su a fadin kasar ta Sin, ya kai sama da dubu 4 da dari 8. A cikinsu kuma, kaso 87 bisa dari ne ake bude kofar su ga jama'a ba tare da karbar kudi ba.

Kana a dai wannan rana, an shirya bikin kafuwar kawancen wuraren adana kayayyakin tarihi na kasashen dake kan hanyar siliki.

Kungiyar wuraren adana kayayyakin tarihi ta duniya ce ta sanya ranar 18 ga watan Mayu na ko wace shekara, a matsayin ranar wuraren adana kayayyakin tarihi ta duniya a shekarar 1977. A wannan rana, wuraren adana kayayyakin tarihin a fadin duniya su kan shirya bukukuwa iri iri, domin tunawa da ranar, da kuma yada manufofin da suke da alaka da hakan, hakan na kuma baiwa al'ummomin kasashen duniya damar kara fahimtar ma'anar kafuwar wuraren adana kayayaykin tarihi, tare kuma da kara nuna sha'awa kan su.

A shekarar da muke ciki, an shirya bikin tunawa da ranar a babban dakin adana kayayyakin tarihin birnin Beijing, inda shugaban hukumar kula da aikin kare kayayyakin tarihin kasar Sin Liu Yuzhu, ya yi bayani kan ci gaban da kasar Sin ta samu a wannan fanni, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, yana mai cewa, "Ya zuwa karshen shekarar 2016, adadin wuraren adana kayayyakin tarihin da aka yi rajista a fadin kasar Sin ya kai 4873, adadin da ya karu da 181, idan aka kwatanta da na shekarar 2015. Kana tsarin gudanar da harkokin wuraren adana kayayyakin tarihin kasar Sin ya samu kyautatuwa yadda ya kamata.

Abu mai faranta ran mutane shi ne adadin wuraren adana kayayaykin tarihi iri na sana'o'i, da kuma irin na masu zanan kansu ya karu cikin sauri. A halin da ake ciki yanzu, adadin wuraren adana kayayyakin tarihin da masu zaman kansu suka kafa ya kai kaso 26.6 bisa dari, idan aka kwatanta da na daukacin adadin wuraren adana kayayyakin tarihi a fadin kasar ta Sin.".

Babban jami'in kungiyar wuraren adana kayayaykin tarihin duniya Peter Keller ya bayyana cewa, taken ranar wuraren adana kayayyakin tarihin duniya ta bana ita ce "wuraren adana kayayyakin tarihi, da tarihi: wuraren adana kayayyakin tarihi suna nunawa jama'a tarihin duniya.". Ya ce makasudin tsara wannan take shi ne domin tunatar da jama'ar kasashen duniya, game da waiwayen tarihi, tare kuma da kara fahimtar al'adun duniya. A karshe dai za a kago wata makomar bil adama mai haske.

Ban da haka kuma, ana iya cewa, taken ya dace da amfanin samar da hidima na wuraren adana kayayyakin tarihi, Peter ya ce, "Har kullum ana tattaunawa kan amfanin samar da hidima a wuraren adana kayayyakin tarihi, ana fatan wuraren adana kayayyakin tarihi za su taka rawa wajen nunawa jama'a al'adun tarihi, da kuma sa kaimi kan aikin ba da ilimi. Kana ana sa ran cewa, 'yan kallo za su iya kara nuna sha'awarsu ga duniya ta hanyar kallon kayayyakin da ake nunawa a wuraren adana kayayyakin tarihi."

Shugaban hukumar kula da aikin kare kayayyakin tarihin kasar Sin Liu Yuzhu, shi ma ya bayyana cewa, yanzu haka a kasar Sin, an bude kofar wuraren adana kayayyakin tarihi da kusan kaso 90 bisa dari ga jama'a ba tare da karbar kudi ba. Liu Yuzhu yana mai cewa, "Gaba daya wuraren adana kayayyakin tarihin da yawansu ya kai 4246, suna budewa kofa ga jama'a ba tare da karbar kudi ba a nan kasar Sin, adadin da ya kai kaso 87.1 bisa dari, idan aka kwatanta da daukacin wuraren dake fadin kasar. Kana a cikin 'yan shekarun da suka gabata, ko wace shekara, ana shirya nune-nune a wannan fanni sama da dubu 30. Ban da haka kuma, adadin ayyukan yada manufofin da ake shiryawa game da wannan batu ya kai kusan dubu 110 a fadin kasar. Kaza lika adadin jama'ar da suka shiga ayyukan ya kai wajen miliyan 900."

Wurin adana kayayyakin tarihi gada ce, dake hada tarihi da makomarmu, kuma gada ce da ta hada kasar Sin da sauran kasashen duniya. Wannan rana, an kafa ta da kawancen wuraren adana kayayyakin tarihin duniya na kasashen dake kan hanyar siliki. Kuma kawo yanzu, kasashen da suka shiga kawancen sun haura goma, kana wuraren adana kayayyakin tarihin da suka shiga kawancen sun haura 50. Ko shakka babu adadin zai karu a kai a kai.

Shugaban kawancen Wang Bin ya bayyana cewa, kawancen da aka kafa zai sa kaimi ga ci gaban cudanya da hadin gwiwa a fannin al'adu, a tsakanin wuraren adana kayayyakin tarihi na kasashen da suka amince da shawarar "ziri daya hanya daya". (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China