in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawarar "Ziri daya da hanya daya" ta taimakawa Afirka wajen kara cudanya da juna
2017-06-06 13:24:02 cri

A cikin 'yan kwanaki kadan bayan da aka kaddamar da layin dogo a tsakanin birnin Nairobi, hedkwatar mulkin kasar Kenya da birnin Mombasa, mai tashar jiragen ruwa mafi girma a kasar, layin dogon ya samu karbuwa sosai daga wajen jama'ar kasar, har ma an sayar da dukkan tikitin shiga jirgin.

A matsayin wani muhimmin shiri da aka aiwatar a Afirka bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya", layin dogo a tsakanin Mombasa da Nairobi wato SGR ya zama wani kyakkyawan shaida wajen cimma burin samun bunkasuwa bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya", lamarin da ya kara shaida cewa, shawarar ta dace da yanayin bunkasuwa da ake ciki yanzu, gami da muradun jama'ar kasa da kasa.

Kamfanin shimfida hanyoyi da gadoji na kasar Sin shi ne ya kula da aikin shimfida layin dogo na SGR, wanda aka kaddamar da shi a ranar 31 ga watan jiya, kana aka fara yin sufurin fasinjoji daga ranar 1 ga wata. A halin yanzu dai, akwai jirgin kasa daya daga Mombasa zuwa Nairobi, sa'an nan akwai daya daga Nairobi zuwa Mombasa a kowace rana.

Bisa kididdigar da hukumar ba da umurni kan aikin layin dogo na SGR ta bayar, an ce, a ranar 4 ga wata, yawan fasinjojin da suka dauki jirgin kasa mai lamba E1 daga Mombasa zuwa Nairobi ya kai 1366, sannan akwai wasu daruruwan mutane da ba su samu tikiti ba. A wancan rana kuma, fasinjoji 1219 ne suka dauki jirgin kasa mai lamba E2 daga Nairobi zuwa Mombasa.

Dalilin da ya sa layin dogo na SGR ya samu karbuwa sosai shi ne sabo da an rage rabin yawan kudi da tsawon lokacin tafiya duka. Yadda wasu fasinjoji ba su samu damar sayen tikiti ba ya kuma shaida cewa, jama'ar Kenya har da na kasashen Afirka na bukatar yin tafiya cikin sauri sosai.

Madam He Wenping, manazarciya kan harkokin Afirka a cibiyar nazarin kimiyyar zamantakewar al'umma ta Sin ta bayyana cewa, kaddamar da layin dogo na SGR wani labari ne mai dadin ji da aka samu bayan da aka kammala taron koli kan hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" ba da dadewa ba, lamarin da ke da babbar ma'ana.

Haka kuma Macharia Munene, wani masani na kasar Kenya yana ganin cewa, Kenya wata muhimmiyar kasa ce a nahiyar Afirka da ta amsa shawarar "Ziri daya da hanya daya". Ana sa ran ganin yadda za a kaddamar da dimbin shirye-shirye bisa wannan shawarar a Kenya, ta yadda kasar za ta samu dauwamammen ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'ummarta.

Yayin da Chen Yun, mataimakin manaja na kamfanin raya hanyoyin zirga-zirga na kasar Sin ke zantawa da wakilinmu, ya bayyana cewa, aikin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a fannonin layin dogo da hanyar mota da zirga-zirgar sararin sama da ma masana'antu, musamman ma aikin shimfida layin dogo, wani aiki ne mai matukar muhimmanci, kuma ba shakka zai shafi dimbin shirye-shirye.

Ban da gabashin nahiyar Afirka, kasar Najeriya da ke yammacin nahiyar ita ma na da bukatar raya layin dogo, kana tana da fatan samun goyon baya ta fuskar kudi daga wajen kasar Sin. Layin dogo a tsakanin Abuja da Kaduna da kamfanin kasar Sin ya taimaka wajen gina shi, an riga an kaddamar da shi a watan Yuli na bara. Kasancewarsa matakin farko na shirin shimfida layin dogo na zamani da Sin da Najeriya suka rattaba hannu a kai, za a ci gaba da raya shi domin ya kai ga yankuna masu yawa.

Bugu da kari, Madam He Wenping ta furta cewa, a halin yanzu, jimillar ciniki a tsakanin kasashen Afirka ba ta da yawa, wani muhimmin dalilin da ya sa hakan shi ne sabo da muhimman ababen more rayuwa na kasashen Afirka a fannin cudanyar juna ba su samu bunkasuwa sosai ba, wanda kuma ya kawo cikas wajen jawo jarin waje. Sabo da haka, raya muhimman ababen more rayuwa don kara cudanyar juna yana daga cikin abubuwan da ake bukata wajen raya kasuwanci maras kaidi, hade da sassan hada hadar kasuwanci da kulla alaka tsakanin al'ummu.

Madam He ta kuma nuna cewa, wani babban abun da aka tanada cikin shawarar "ziri daya da hanya daya" shi ne sa kaimi ga raya muhimman ababen more rayuwa da kara cudanyar juna. Aikin kuwa ba kawai ya shafi kasashen da ke da nasaba da shawarar ba, dukkan kasashen Afirka ma za su sa hannu a cikinsa.

Yayin da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ziyarci kasashen Mauritania, Cape Verde, Mali da Cote d'Ivoire a watan jiya, ya bayyana cewa, dukkan wadannan kasashen Afirka sun sa hannu cikin ayyukan da shawarar "ziri daya da hanya daya" ta shafa, wanda ya sheda burin nahiyar Afirka na shiga a dama da su. Ya kuma kara da cewa, tarihi ya nuna cewa, dimbin kasashen Afirka na da alaka da hanyar siliki ta teku, don haka muddin suka amince da shawarar, to za su iya hadin gwiwa tare da kasar Sin wajen samun ci gaba.

A nasa bangaren, jakadan kasar Sin dake Kenya Liu Xianfa yana ganin cewa, bayan da aka kammala aikin gina layin dogo na SGR, Sin da Kenya na hada kansu wajen gaggauta aiwatar da shirin shimfida layin dogo tsakanin Nairobi da Malaba, da gina tashar jiragen ruwa ta Lamu. Ta wadannan ayyukan, ana sa ran Afirka za ta kara amincewa da shawarar "ziri daya da hanya daya", wadda za ta ingiza ci gaban Afirka da zamanintar da ita, a kokarin amfana wa jama'ar nahiyar. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China