in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana gudanar da hadin gwiwar kimiyya da fasaha tsakanin Sin da Afirka bisa shawarar "ziri daya hanya daya" yadda ya kamata
2017-05-22 11:01:43 cri

An gudanar da babban taro karo na 21 kan ilmin nau'o'in tsirrai na wurare masu zafi dake nahiyar Afirka a Nairobin kasar Kenya tsakanin renakun 15 zuwa 19 ga wannan wata, sashen adana kayayyakin tarihi na kasar Kenya da jami'ar Nairobi ne suka shirya wannan babban taro karkashin taimakon cibiyar nazarin kimiyya da fasaha ta hadin gwiwar Sin da Afirka dake karkashin jagorancin cibiyar nazarin kimiyya da fasaha ta kasar Sin, ana ganin cewa, babban taron sabon hadin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha ne dake tsakanin Sin da kasashen Afirka bisa shawarar "ziri daya hanya daya".

Ga karin bayanin da abokiyar aikinmu Jamila za ta gabatar.

A nahiyar Afirka, akwai tsirrai na yankuna masu zafi iri daban daban, har suna iya jawo hankulan masu aikin nazarin tsirrai a fadin duniya, a saboda haka wannan babban taron ya samu mahalartarsa sama da dari biyar da suka zo daga kasashe fiye da talatin. Darektan cibiyar nazarin kimiyya da fasaha ta hadin gwiwar Sin da Afirka dake karkashin jagorancin cibiyar nazarin kimiyya da fasaha ta kasar Sin Wang Qingfeng ya bayyana cewa, babban taron yana da ma'ana matuka, yana mai cewa, "A takaice dai, ana iya cewa, makasudin shirya wannan babban taro shine, domin tattauna batutuwa game da yadda za a kare da kuma kyautata albarkatun tsirrai a nahiyar Afirka a nan gaba. Yanzu muna amfani da tsirrai a ko da yaushe a cikin zaman rayuwarmu na yau da kullum, shi ya sa ba ma kawai ana bukatar yin kokarin kare tsire-tsire bane, har ma batun yana shafar sauran batutuwa da dama, misali tsaron abinci, da muhalli mai tsabta, da samar da magungunan sha daga tsirrai, a saboda haka, taron ya jawo hankulan jama'a matuka."

Babban shehun malamin dake aiki a sashen adana kayayyakin tarihin kasar Kenya, kana shugaban babban taron karo na 21 kan ilmin nau'o'in tsirrai na wurare masu zafin dake nahiyar Afirka Geoffrey Mwachala, yana ganin cewa, cibiyar nazarin kimiyya da fasaha ta hadin gwiwar Sin da Afirka dake karkashin jagorancin cibiyar nazarin kimiyya da fasaha ta kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a yayin babban taron da aka gudana kwanakin baya ba da dadewa ba. Yana mai cewa, "Cibiyar nazarin kimiyya da fasaha ta hadin gwiwar Sin da Afirka dake karkashin jagorancin cibiyar nazarin kimiyya da fasaha ta kasar Sin ta samar da yawancin kudaden da ake amfani da su domin shirya wannan taro, kana ta samar da taimakon kudi ga daliban Kenya domin su je jami'o'in kasar Sin don koyon ilmin tsirrai, ana iya cewa, irin wannan hadin gwiwa yana da babbar ma'ana, saboda zai daga matsayin nazarin kimiyya da fasaha na kasashen Afirka, wanda kuma ya dace da manufar shawarar 'ziri daya hanya daya' da gwamnatin kasar Sin ta gabatar."

Gwamnatin kasar Sin ce ta kafa cibiyar nazarin kimiyya da fasaha ta hadin gwiwar Sin da Afirka reshenta a jami'ar koyar da ilmin kimiyya da fasaha game da aikin gona ta Jomo Kenyatta ta kasar Kenya, wadda ta kasance muhimmin dandalin hadin gwiwa ne dake tsakanin Sin da Kenya, wajen kare nau'o'in tsirrai, da sa ido kan muhallin hallitu, da aikin gona na zamani da dai sauransu. Shugaban cibiyar Wang Qingfeng, yana ganin cewa, aikin da cibiyar ke yi mataki ne da aka dauka yayin da ake kokarin tabbatar da manufar shawarar "ziri daya hanya daya", yana mai cewa, "Kenya tana taimakawa matuka yayin da ake kokarin tabbatar da manufar shawarar 'ziri daya hanya daya' a nahiyar Afirka, cibiyar da aka kafa a kasar ta Kenya ita ma tana taka muhimmiyar rawa, musamman ma a fannonin hadin gwiwar tattalin arziki da gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a a Afirka, misali samar da goyon baya wajen kimiyya da fasaha ga aikin gina layin dogo dake tsakanin Mombasa da Nairobi, kana ana fatan dandalin zai samar da taimako wajen horas da kwararru kimiyya da fasaha na kasashen Afirka, ban da haka kuma, ana sa ran cewa, dandalin zai taimakawa kasashen Afirka wajen kyautata sharadin gudanar da aikin nazarin kimiyya da fasaha."

A watan Aflilun bana, an buga littafin "Nau'o'in tsirran kasar Kenya" da na "Hotunan labarin kasa na Kenya" a kasar ta Kenya, masana kimiyya da fasaha na cibiyar nazarin kimiyya da fasaha ta hadin gwiwar Sin da Afirka dake karkashin jagorancin cibiyar nazarin kimiyya da fasaha ta kasar Sin ne suka tsara wadannan littattafai bayan kokarin da suka yi, Wang Qingfeng ya bayyana cewa, "An rubuta littafin 'nau'o'in tsirran kasar Kenya' ne bayan da aka yi nazari sosai kan tsirrai na kasar Kenyan, zai taimaka matuka wajen raya tattalin arzikin kasar da kuma kare muhalli a kasar, ko shakka babu yana da babbar ma'ana, muna fatan za mu kara samar da taimako ga ci gaban kasashen Afirka, musamman ma a fannin kimiyya da fasaha." (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China