Haka kuma, akwai wasu shirye-shirye guda biyu da kasar Sin ta gabatar wa bankin, wadanda suka hada da shirin kyautata yanayin kogin Xiang dake lardin Hunan na kasar Sin da kuma shirin tsimin makamashi na lardin Jiangxi. Sauran shirye-shirye guda biyu da bankin ya zartas su ne, shirin samar da ruwa mai tsafta ga manoma kimanin miliyan 3 dake zaune a kauyuka sama da dubu 3, wanda kasar Indiya ta gabatar, shirin da aka yi hasashen cewa, zai lashe dallar Amurka miliyan 470. Haka kuma akwai shirin kyautata tsarin shari'a da kasar Rasha ta gabatar, wanda zai lashe dallar Amurka miliyan 460.
Shugaban bankin raya kasashen BRICS K.V.Kamath ya bayyana cewa, wadannan shirye-shirye guda hudu sun dace da kokarin da ake da shi na biyan bunkasuwar mambobi kasashen BRICS, a sa'i daya kuma, sun nuna aniyar bankin na karfafa ayyukan dake shafar neman dauwamammen ci gaba. Bugu da kari, a nan gaba, bankin zai ci gaba da mai da hankali a kan shirye-shiryen da za su kyautata zaman rayuwar al'umma. (Maryam)