in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar IS ta dauki alhakin harin birnin Aden na kasar Yemen
2016-12-19 10:20:24 cri
A jiya Lahadi ne aka kaddamar da harin kunar bakin wake a birnin Aden na kasar Yemen, wani ma'aikacin lafiya a asibitin gwamnatin dake birnin Aden ya bayyana cewa, an kai gawawwakin mutane 49 zuwa asibitin, kana ana ba da jinya ga mutane a kalla 39 da suka samu raunuka a sakamakon harin.

Kungiyar IS ta wallafa a shafinta na Twitter a jiya Lahadi cewa, ita ce ke da alhakin kai wannan hari, wanda ya shirya kai harin shi ne Abu Hashim Radfani.

An bayyana cewa, 'dan kunar bakin wakin ya tada bom din dake jikinsa ne a gaban wani gini, a lokacin da sojojin gwamnatin kasar suka taru domin amsar kudadensu na albashi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China