A Juma'ar da ta gabata, kasar Sin ta nuna goyon bayanta ga halastacciyar gwamnatin kasar Yemen, kana ta nuna kin amincewa da yunkurin kafa gwamnatin bangare daya wacce ka iya dagula halin da ake ciki a kasar.
Tsagin mabiya 'yan tawayen Houthi da na tsohon shugaban kasar Ali Abdullah Saleh, sun sanar da cewa za su kafa gwamnatin kwato 'yancin kasar, matakin da suka dauka ba tare da amincewar halastacciyar gwamnatin kasar wanda kuma kasashen duniya suka amince da ita ba.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana cewa, ba sa goyon bayan yunkurin kafa gwamnatin wariya wanda za ta iya haifar da tabarbarewar al'amura a kasar, kuma wannan hanya ba za ta haifar da maslaha wajen warware rikicin siyasa da ya dabaibaye kasar ba.
Mista Geng, ya bukaci bangarorin da abin ya shafa da su cigaba da tattaunawar sulhu da nufin warware banbance banbancen da ake fama da shi a kasar, tare kuma da tabbatar da cimma matsaya kan wata yarjejeniya wadda dukkanin bangarorin kasar za su iya amincewa da ita, karkashin shirin zaman lafiya na majalisar hadin kai ta GCC da sauran yarjejeniyoyi na kwamitin tsaron MDD.(Ahmad Fagam)