in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan Afirka 30 sun rasu sakamakon wani harin sama a gabar tekun Yemen
2017-03-17 19:59:59 cri
Wata majiyar jami'an tsaro a Yemen, ta ce wasu bakin haure 'yan Afirka dake kan hanyar su ta komawa gida kimanin su 30 sun gamu da ajalin su, bayan da wani jirgin saman yaki ya kai musu farmaki a gabar tekun yammacin kasar ta Yemen.

Majiyar ta ce mutanen dake cikin wani jirgin ruwa na shirin komawa kasashen Sudan, da Somalia da ma wasu sauran kasashen Afirka ne, lokacin da wani jirgin yaki da ake zaton na dakarun hadin gwiwar da Saudiya ke jagoranta ne ya yi musu luguden wuta. An dai ce wasu daga mutanen da ke jirgin sun kubuta, yayin da wasu masu aikin ceto suka kai musu dauki bayan aukuwar farmakin.

A daya hannun kuma wasu kafofin labarai na wurin, sun ce su ma wasu masunta dake kamun kifi a gabar tekun kasar ta Yemen sun hallaka, sakamakon wannan harin ta sama.

Cikin 'yan makwannin nan dai dakarun da Saudiyya ke jagoranta na matsa kaimin kaddamar da hare hare, a wani mataki na tallafawa gwamnatin kasar ta Yemen, cin galabar yakin da ta ke yi da 'yan tawayen Houthi, musamman a sassan gabar ruwan kasar dake Hodyada.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China