Wani jami'in soja da ya bukaci a sakaye sunansa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin, Xinhua cewa, fadan ya barke ne a kusa da maboyar mayakan na al-Qaida da ke yankin, inda aka kwashe sama da sa'o'i biyu ana bata kashi.
Wata majiyar asibiti ta tabbatar da cewa, mayakan al-Qa'ida fiye da 13 da kuma sojojin gwamnati 10 ne aka kashe a yayin arangama tsakanin bangariorin biyu.
A wani labarin kuma, wasu da ake zargin mayakan al-Qaida ne sun jikkata sojojin gwamnatin kimanin 8, bayan da suka yiwa wasu motocin sojojin gwamnati kwanton bauna a garin Shoqra da ke lardin Abyan.
Sai dai kuma a 'yan watannin da suka gabata sojojin da ke samun goyon bayan gwamnati sun kaddamar da hare-haren yaki da 'yan ta'adda, inda suka fatattaki mayakan dake da alaka da al-Qa'ida da mayakan IS da ke Yemen daga muhimman yankuna da wuraren gwamnati da ke lardunan Lahj da Abyan.
Tun a watan Maris na shekarar 2015 , al'amuran tsaro suka tabarbare a kasar Yemen,lokacin da fada ya barke tsakanin kungiyar Houthi ta 'yan mas'habar shi'a wadda ke samun goyon bayan tsohon shugaban kasar Ali Abdallah Saleh da gwamnatin kasar wadda ke samun goyon bayan kawancen kasashen Laraba karkashin jagorancin kasar Saudiya.
Mutane sama da dubu 10 ne suka halaka, rabinsa fararen hula, tun lokacin da aka kaddamar da hare-hare ta kasa da ta sama a kasar.(Ibrahim)