in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#BRICS# Xi Jinping: karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, tare da kafa salon "BRICS+"
2017-09-05 14:08:37 cri
A yayin wani taro na manema labaru da ya gudana da tsakar ranar Talatar nan 5 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, taron ganawa tsakanin shugabannin kasashen BRICS, da taron tattaunawa tsakanin kasashen da tattalin arzikinsu ke samu saurin bunkasuwa, da kasashe masu tasowa, sun alamta cewa karfi da ake da shi na karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, da ma mataki na kasashen duniya baki daya.

Dukkan shugabanni wadanda suka halarci taron tattaunawar na ganin cewa, ya kamata kasashen da tattalin arzikinsu ke samu saurin bunkasuwa, da kasashe masu tasowa, su taka karin rawa wajen tabbatar da ajandar neman dawaumammen ci gaba har zuwa nan da shekara ta 2030, da kyautata tsarin tattalin arzikin duniya, ta yadda za a iya karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa da kafa salon BRICS+. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China