in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin watsa labarun Afirka ta kudu sun bayar da rahoto kan jawabin Xi Jinping a gun taron shugabannin BRICS
2017-09-05 10:09:36 cri
Muhimman kafofin watsa labaru da dama na kasar Afirka ta kudu, sun gabatar da rahoto kan jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi a gun taron shugabannin kasashen BRICS. Ciki kuwa hadda sanarwar da shugaba Xi ya bayar game da shirin kasarsa na ba da kudin Sin RMB miliyan 500, bisa matakin farko don bunkasa hadin kai, da yin cudanya a fannonin tattalin arziki, da fasaha tsakanin kasashen BRICS, da kuma kudurin ba da kudi har dalar Amurka miliyan 4, a matsayin kudin ajiya a sabon bankin raya kasashen na BRICS, rahotannin da suka jawo hankulan kafofin watsa labarun Afirka ta kudu kwarai.

A jiya Litinin, kafar yanar gizon ta SABK dake Afirka ta kudu, ta bayar da rahoto mai taken 'Sin ta yi alkawarin kara tallafawa sabon bankin raya kasashen BRICS'. Rahoton ya yi bayani kan jawabin shugaba Xi, inda aka bayyana yadda bankin ke samun tallafin kudi, kana aka mai da hankali kan kudurin da Sin ta tsaida, na samar da dalar Amurka miliyan 4 ga aikin ajiyar kudi na bankin. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China