in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya bukaci hadin kai tsakanin kasashen da arzikin su ke bunkasa da masu tasowa
2017-09-05 09:23:37 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya bukaci kasashe da arzikin su ke samun saurin bunkasuwa, da kasashe masu tasowa, da su hada kai da juna domin samun ci gaba.

Shugaba Xi ya yi wannan kira ne a ranar Litinin, cikin jawabin sa yayin liyafar da aka shiryawa mahalarta taro na 9 na kungiyar BRICS, da taron tattauna batutuwan da suka shafi cinikayya da ci gaban kasashe masu tasowa, wanda ya gudana a birnin Xiamen dake kudu maso gabashin kasar Sin.

Shugaba Xi ya kwatanta birnin Xiamen da wata kafa ta bude kofofin kasar Sin, kuma birni da ke da damammaki na bunkasa kirkire kirkire. Ya ce, taron na wannan karo da ya samu halartar shugabanni na kasashe masu samun ci gaba da masu tasowa, zai baiwa birnin Xiamen damar kafa wani tarihi na ci gaba.

Shugaban na Sin ya kara da cewa, duk da irin nisa dake tsakanin kasashe mahalarta taron, mafarki iri daya, da burin samun ci gaba ya sanya su kasancewa aminai kuma abokan hulda na kusa.

Daga nan sai ya tabbatar da cewa, muddin dai kasashen da tattalin arzikin su ke bunkasa cikin sauri, da kasashe masu tasowa sun hada karfi da karfi wajen taimakon juna, ba shakka za su kai ga cimma nasara mai kama da sauya turbaya zuwa zinari. Za kuma su sada al'ummun su da alherai masu tarin yawa, ta yadda za su yi rayuwa mai inganci cikin wadata da annashuwa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China