in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci shawarari tsakanin shugabannin kasashen BRICS da majalisar masana'antu da cinikayya na kungiyar
2017-09-04 20:14:01 cri
A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci shawarwari tsakanin shugabannin kasashen BRICS da majalisar masana'antu da cinikayya ta kungiyar da ya gudana a birnin Xiamen dake kasar Sin tare da yin jawabi.

Bayan da ya saurari rahoton da wakilan majalisar masana'antu da cinikayya ta kungiyar da na sabon bankin raya kasa na kungiyar suka gabatar, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, shugabannin kasashen kungiyar BRICS sun amince da ci gaba da hada kai a shekaru 10 masu zuwa, don daga matsayin hadin gwiwarsu zuwa wani sabon matsayi. Yana fatan hukumomin biyu za su yi amfani da wannan dama tare da hada kai don samun babban ci gaba a fannoni 3, wato sa kaimi ga kasashen BRICS don moriyar juna, da taimakawa kasashen don ci gaban tattalin arziki, da kuma yin mu'amala a tsakanin al'ummominsu.

A yau din ne kuma, shugabannin kasashen BRICS suka halarci bikin bude bukukuwan al'adun kasashen BRICS da kuma bikin nune-nunen hotunan al'adun kasashen. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China