in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin MDD ya ziyarci Misrata na kasar Libya don tattaunawar sulhu
2017-08-16 10:57:32 cri
Sabon wakilin MDD a kasar Libya Ghassan Salame, ya ziyarci Misrata, birni na uku mafi girma a kasar Libya a ranar Talata, domin halartar taron tattaunawa da shugabannin al'umma da na siyasa na birnin.

Salame, wakilin musamman na sakatare-janar na MDD kuma shugaban tawagar kiyaye zaman lafiya ta MDD a Libya, ya gana da shugabannin majalisar gudanar da mulki ta Misrata, da shugabannin al'umma da kuma daliban jami'ar Misrata, kuma sun tattauna ne game da irin bukatun da birnin ke da su da makomar ci gaban birnin.

Salame, ya yaba da irin kokarin da birnin na Misrata ke yi wajen yaki da ta'addanci, da kokarin tabbatar da hadin kan birnin, da tabbatar da 'yancin mulkin kasar ta Libya. Ya nanata cewa, Libya za ta ci gaban da kasancewa a matsayin kasa, duk da irin kalubalolin dake addabarta.

Salame ya maye gurbin Martin Kobler, wanda ya jagoranci tattaunawar sulhu ta hanyar siyasa tsakanin 'yan tawayen Libya, lamarin da ya haifar da kafa gwamnatin hadin kan kasa.

Sai dai kuma, har yanzu kasar na fama da rarrabuwar kai, sakamakon tabarbarewar tsaro da tashe-tashen hankula. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China