in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarori daban daban na Afirka ta kudu suna sa rai kan tattaunawar BRICS
2017-09-04 10:01:32 cri
Shugaban Afirka ta kudu Jacob Zuma, ya bayar da wata sanarwa gabanin tashi zuwa birnin Xia'men na kasar Sin don halartar taron BRICS, inda ya bayyana cewa, kasarsa na tsayawa kan ganin cewa, tsarin kungiyar BRICS zai tallafawa Afirka ta kudu, wajen warware manyan matsaloli guda uku da kasar ke fuskanta, ciki har da fama da talauci, da rashin aikin yi da kuma rashin daidaito tsakanin al'umma. Kaza lika hakan zai taka muhimmiyar rawa wajen cimma burin samun ci gaban kasashe masu tasowa.

Game da haka, daraktan cibiyar nazarin harkokin kasashen BRICS, na kwamitin nazarin fasahar al'adu na kasar Afirka ta kudu Jaya Josie ya bayyana cewa, yana sa ran ganin za a kafa hukumar wani sashi na auna nasarar ayyuka. Ya ce hakan zai iya zama tallafi ga tsarin auna nasarori da ake da su a mataki na kasa da kasa.

Baya ga haka, daraktan ya bayyana fatansa na ganin an karfafa hadin kai a fannin cinikayya tsakanin kasashen BRICS. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China