in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta kudu za ta karbi bakuncin taron BRICS na badi
2017-09-04 09:29:52 cri

Kasar Afirka ta kudu ce za ta karbi bakuncin taron kungiyar BRICS karo na 10 da za a gudanar badi. Da yake tabbatar da hakan, yayin taron harkokin kasuwanci da aka bude jiya Lahadi a birnin Xiamen na lardin Fujian dake nan kasar Sin, shugaban Afirka ta kudun Jacob Zuma, ya ce kasarsa na da cikakkun damammaki na guraben zuba jari, da fadadar tattalin arziki da ci gaba.

Don haka a cewarsa Afirka ta kudu za ta kara zurfafa hadin gwiwa da sauran kasashe mambobin kungiyar BRICS a fannin kasuwanci. Shugaba Zuma ya kara da cewa, daukacin nahiyar Afirka na daf da shiga wani sabon mataki na samun ci gaba mai dorewa. Daga nan sai ya bayyana fatan hallarar dukkanin mambobin kungiyar da sauran mahalarta taron na badi a kasarsa.

A shekarar 2016 da ta gabata, yawan kudaden cinikayya tsakanin Afirka ta kudu da sauran kasashen mambobin kungiyar BRICKS, ya kai dalar Amurka biliyan 31.2, kamar dai yadda shugaba Zuman ya bayyana.

Taron na yini biyu na masu ruwa da tsaki kan harkokin kasuwanci, wanda ya gudana gabanin taron shugabannin kungiyar BRICS, ya samu halartar wakilan kamfanoni sama 600. Kuma taron wani jigo ne, cikin manyan ayyukan da a kan shirya a yayin taron kungiyar na shekara-shekara. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China