#BRICS# Shugaba Xi jinping ya ba da jawabi a yayin taron dandalin harkar masana'antu da cinikayya na kasashen BRICS

Da yammacin yau agogon kasar Sin ne aka bude taron dandalin harkar masana'antu da cinikayya na kasashen BRICS a birnin Xiamen, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi mai lakabi "A kokarta don inganta hadin kan kasashen BRICS cikin shekaru goma masu zuwa". Shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 20 da kafuwar tsarin hadin kan kasashen BRICS, don haka taron dandalin harkar masana'antu da cinikayya na kasashen BRICS na bana ya jawo hankalin mutane sosai. A cikin jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ya bayyana cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, kasashen BRICS sun yi namijin kokari wajen neman bunkasuwa tare, sa'an nan sun inganta hadin gwiwar su don moriyar juna, baya ga sauke nauyi da ke wuyansu don ba da gudummowarsu ga fadin duniya.
Shugaba Xi ya jaddada cewa, hadin gwiwar kasashen BRICS na cikin wani muhimmin lokaci, wadanda ke fuskantar muhimman ayyukan da suka kunshi raya tattalin arziki da karfafa hadin gwiwa tsakaninsu. Ya ce ya kamata kasashen su kiyaye manufar hadin kan tattalin arziki, su kuma aiwatar da tsare-tsaren hadin gwiwa na kungiyar, tare da sa kaimi ga inganta tsarin hadin gwiwarsu daga dukkan fannoni.