in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya gana da Putin, inda suka yi kira da a inganta zaman lafiya da ci gaban duniya
2017-09-03 20:40:46 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a yau Lahadi, inda suka yi kira da a hada hannu wajen inganta zaman lafiya da ci gaban duniya.

Shugaba Putin na birnin Xiamen dake kudu maso gabashin kasar Sin don halartar taron kungiyar BRICS karo na 9 da aka shirya gudanarwa tsakanin yau 3 zuwa 5 ga watan nan da muke ciki.

Shugaba Xi ya ce yana fatan Vladimir Putin zai ji dadin ziyararsa a Xiamen, yana mai imanin za su shiga shekaru 10 na kungiyar masu tarin nasarori.

Wannan dai shi ne karo na 4 da shugabanin biyu ke haduwa a bana. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China