A cikin jawabinsa, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ce, kasarsa ta samu nasarar gudanar da taron dandalin tattaunawar koli na hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa bisa gudanar da shawarar "ziri daya da hanya daya" a watan Mayun bana. Shawarar tana samar da wani dandalin yin hadin gwiwar ta a-zo-a-gani tsakanin kasashen duniya, wadda kuma shawara ce da Sin ta gabatar domin samun ci gaba cikin hadin gwiwar kasa da kasa, a kokarin ganin kasashen duniya sun ci gajiyarta. Baya ga haka, gudanar da shawarar "ziri daya da hanya daya" za ta samar wa kasashen duniya sabon dandalin yin hadin gwiwa da samun nasara, tare da samar da sabon zarafi na aiwatar da muradun samun ci gaba mai dorewa da ake son cimmawa kawo shekarar 2030. (Tasallah Yuan)