in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadarin wani jirgin saman koyon tuki a Nijeriya, ya yi sanadin mutuwar matukin jirgin
2017-08-25 09:53:43 cri

Wani jirgin saman koyon tuki mallakar rundunar sojin saman Nijeriya, ya yi hadari a mazaunin kwalejin horas da sojoji ta kasar na din din din dake jihar Kaduna a arewacin kasar.

Hadarin ya auku ne da misalin karfe 4:25 na yammacin jiya Alhamis, inda ya yi sanadin mutuwar matukin jirgin.

Kakakin rundunar sojin saman Air Commodore Olatokunbo Adesanya da ya tabbatar da aukuwar hadarin ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce matukin ne kadai a cikin jirgin.

Ba a san musababbin hadarin ba, sai dai babban hafsan sojin saman ya ba da umarnin nan take, na kafa kwamitin bincike don tantance sanadin hadarin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China