Lai Mohammed wanda ya bayyana hakan a birnin Abuja fadar mulkin kasar, yayin wani taron masu ruwa da tsaki da hukumar kula da kafafen watsa labaran kasar NBC a jiya Alhamis, ya ce wannan mataki daya ne daga manufofin da gwamnatin kasar ke dauka na dakile kalaman batanci.
Ministan ya kara da cewa, wasu daga kafafen Radio a fadin kasar na yada shirye shirye da ka iya rura wutar rikici, irin matakan da su ne suka kunna wutar kisan kiyashi da ya auku a kasar Rwanda cikin shekarar 1994, lamarin da ya haddasa kisan fararen hula har 800,000 cikin kwanaki 100 kacal.
Don haka sai ya ja hankalin hukumar NBC da kada ta yi kasa a gwiwa, wajen yaki da matsaloli masu alaka da yaduwar kalaman kiyayya a tsakanin al'ummar Najeriya.(Saminu Alhassan)