Wata sanarwar da ta shiga hannun kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya, ta ce Sanata Coons wanda mamba ne a kwamitin majalisa kan kasafin kudi da harkokin waje da shari'a da kananan sana'o'i da tabbatar da da'a, shi ne na jagorancin ayarin.
Baya ga Nijeriya, ayarin zai kuma kai ziyara kasashen Ghana da Cote d'Ivoire da Gambia a wani bangare na rangadin da yake a yammacin Afrika.
Yayin ziyarar tasu a Nijeriya da za ta kasance tsakanin ranar 28 zuwa 31 ga wannan wata, jami'an na Amurka za su gana da shugabanni dan kara yaukaka huldar dake tsakanin kasashen biyu.
Daga cikin batutuwan da jami'an za su tattauna kai, har da yaki da kungiyar Boko Haram da kuma yanayin agajin jin kai a arewa maso gabashin Nijeriya.
Za kuma su kai ziyarar cibiyar harkokin kasuwanci ta Nijeriya wato Lagos, inda za su tattauna kan harkokin cinikayya da zuba jari. (Fa'iza Mustapha)