A cewarsa, za a yi kokarin samun nasarori ta fuskar hadin gwiwar kasashen BRICS cikin shekaru 10 masu zuwa. Don cimma wannan buri, da farko, za a zurfafa hadin gwiwar kasashen don taimakawa kokarin raya tattalin arzikinsu. Na biyu, za a kara daukar nauyin kare zaman lafiya a duniya. Sa'an nan, na uku, za a kyautata tsarin kula da tattalin arzikin duniya. Na hudu kuma shi ne kulla huldar hadin gwiwa da karin wasu kasashe.(Bello Wang)