in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude sabon zauren matafiya a wani filin jirgin saman kasar Sin
2017-09-01 11:05:49 cri
An bude sabon zauren jira na matafiya a filin jirgin saman Wuhan, babban birnin lardin Hubei dake yankin tsakiya na kasar Sin, a lokacin da wani jirgi ya tashi zuwa Chongqing da misalin karfe 7:20 na safiyar jiya Alhamis.

Mataimakin Manajan rukunin filin jirgin saman Hubei Gan Xiangtian, ya ce ana sa ran zauren na 3, na filin jirgin saman kasa da kasa na Wuhan na Tianhe, wanda ya lakume yuan biliyan 40 kwatankwacin dala biliyan 6, zai dauki matafiya miliyan 35 a ko wacce shekara zuwa shekarar 2020.

Sannan kayakin da za a wuce da su ta cikin zauren za su kai ton 440,000 a ko wacce shekara.

Yayin da za a yi wa zaure na 1 da na 2 na filin jirgin saman kwaskwarima don tashin jirage na musamma da masu arahar farashi, za a yi amfani da sabon zauren wajen tafiye-tafiyen da suka shafi na cikin gida da kasashen waje.

Baya ga zauren, an kuma bude sabuwar cibiyar sufuri a filin, wanda ke samar da hanyar jirgin karkashin kasa da ta motocin safa da na tasi.

Filin jirgin saman na Tianhe ya samu fasinjoji miliyan 20.8 a bara, adadin da ya karu da kaso 9.6 a kan na 2015.

Bugu da kari, jirage na tashi daga filin zuwa birane 47 dake kasashe 24. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China