Yau Alhamis 3 ga wata, aka kaddamar da aikin gina tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa ta Baihetan da ke kogin Jinsha. Kana aikin ya kasance a kan gaba a fannoni da dama a duniya, kamar yawan ramukan da ke karkashin kasa da kowane janareto ya iya samar da wutar lantarki kilowatts miliyan daya a kowace awa, suna matsayin farko a duniya. An dauki matakai masu inganci wajen tsara madatsar ruwa da tsayinta ya kai mita 300 a fannin jure matsalar girgizar kasa, kuma girmanta ya kasance a kan gaba a duniya. (Kande Gao)