in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taro tsakanin kasashen BRICS kan yadda za su tafiyar da harkokin mulki
2017-08-18 14:01:25 cri
An kaddamar da wani taron karawa juna sani a jiya Alhamis, tsakanin kasashen BRICS game da yadda za su tafiyar da harkokin mulkin kasa a birnin Quanzhou na lardin Fujian dake kudu maso gabashin kasar Sin. Wasu jami'an gwamnati da kwararru da masana daga kasashen Sin, da Rasha, da Brazil, da Indiya, da Afirka ta Kudu, da Tanzaniya, da Chile da Mexico sun hallara, inda suka yi musayar ra'ayoyi dangane da yadda za'a karfafa hadin-gwiwa don neman ci gaba kafada da kafada.

Babban taken taron karawa juna sanin a wannan karo shi ne, budewa juna kofa, da neman cimma moriya tare. Mataimakin shugaban sashen yayyata ayyukan kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Mista Huang Kunming, ya gabatar da jawabi, inda ya ce, shugabannin kasashe membobin kungiyar BRICS sun cimma matsaya cewa, za su yi musayar ra'ayi kan yadda za su tafiyar da harkokin mulkin kasa, kana, wannan taron da aka yi, wani muhimmin sashi ne na ganawar da za'a yi tsakanin shugabannin kasashen BRICS a birnin Xiamen na kasar Sin a watan Satumban bana.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China