Kamfanin Great Wall dake karkashin rukunin dake nazarin kimiyya da fasahohin sararin samaniya na kasar Sin ya bayyana cewa, Sin ta himmatuwa wajen zurfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasashen duniya a fannin harkokin da suka shafi nazarin sararin samaniya, inda ya zuwa yanzu, aka kammala shirye-shiryen harba taurarin dan Adam har sau 55.
Tun lokacin da aka shiga karni na 21, kamfanin ya gudanar da ayyukan harba taurarin dan Adam, wasu kasashe ciki har da Nijeriya, Pakistan, Belarus, Laos da sauransu sun amfana da hidimar fasahar harba taurarin dan Adam da Sin dake da shi. (Zainab Zhang)