Ana da alkaluma da dama a cikin tsarin taurarun dan Adam na yin binciken yanayi da teku da muhalli da sauransu, idan aka yi amfani da bayanan, za a amfanawa sha'anin bada hidima da rayuwar jama'a. Kamfanin kimiyya da masana'antun sararin samaniya na kasar Sin ya kafa cibiyar tattara alkaluma daga sararin samaniya a ranar 20 ga wata, wadda za ta samar da abubuwan da ake bukata ga gwamnati da kamfanoni ta hanyar tattara da nazarin alkaluman da ta samu da gabatar da su.
Bayanan da aka samu daga sararin samaniya sun taka muhimmiyar rawa a fannonin kiyaye tsaron kasa, raya sana'o'i, kyautata zaman rayuwar jama'a da sauransu.
Shugaban cibiyar tattara alkaluma daga sararin samaniya Ni Jinsheng ya bayyana cewa, kafa cibiyar ya samar da wani dandalin bada hidima da samar da abubuwan da ake bukata ta hanyar tattara alkaluma da yin nazari, ta haka za a daga karfin kasar Sin na sha'anin amfanin bayanan sararin samaniya a duniya. (Zainab)