Tauraron dan adam din samfurin Shijian-13, shine tauraron dan adam na farko da kasar Sin ta harba wanda zai karfafa harkokin sadarwa, kuma an harba shi ne daga cibiyar harba tauraron dan adam ta Xichang dake kudu maso yammacin kasar Sin a jiya Laraba da misalin karfe 7:04 na yamma.
Tauraron dan adam din wanda ke da karfin Gbps 20 zai iya shafe shekaru 15 a duniyar orbit, wanda aka yi amfani da nau'rar harba roka ta Long March-3B.
Wannan sabon tauraron dan adam yana da karfin aikin sadarwa sama da dukkan tauraron dan adama na sadarwa da kasar Sin ta taba harbawa, yana iya samar da karfin yanayin yin amfani da internet a cikin jiragen sama da jiragen kasa masu saurin tafiya, har ma ga yankunan da suke da karancin cigaba.
Babban injiniyan hukumar kimiyya da fasaha domin tsaron kasa ta kasar Sin Tian Yulong, yace harba wannan tauraron dan adam din na daga cikin manufofin kasar Sin na bunkasa fannin fasahar sadarwa.
Ya ce sabanin tauraron dan adam da aka harba a baya wadanda suke amfani da sinadarai a matsayin makamashi, tauraron dan adam samfurin Shijian-13, shine na farko da kasar Sin ta yi amfani da wutar lantarki.