An ce, tauraron dan Adam da aka harba a wannan karo, tauraro ne da za'a yi amfani da shi a fannonin sadarwa, da rediyo, da talabijin da sauransu. Haka kuma, za'a yi amfani da shi wajen gudanar da wasu gwaje-gwajen fasahohin zamani.
Cibiyar nazarin fasahohin harba taurarin dan Adam ta Shanghai ita ce ta samar da wannan tauraron dan Adam wato tauraron dan Adam mai gwajin fasahar sadarwa, yayin da cibiyar nazarin fasahar harba roka ta kasar Sin ta samar da roka samfurin Long March-3B.
Wannan shi ne karo na 245 da roka samfurin Long March ta yi jigilar tauraron dan Adam zuwa sararin samaniya, al'amarin da ya shaida cewa, an cimma nasarar kammala aikin harba tauraron Adam zuwa sararin sama na farko a sabuwar shekara ta 2017.(Murtala Zhang)