Tauraron samfurin Fengyun-4, shi ne na farko da kasar Sin ta kaddamar a karo na biyu na wannan karni wadda kasar ta harba zuwa hanyarsa dake sararin sama, kuma shi ne irinsa na farko da ake iya sarrafa shi ta hanyar amfani da na'urar da ake sarrafa ta daga nesa yayin da yake can sararin samaniya.
A cewar ofishin kula da kimiyya da fasaha da tsaron kasa na kasar Sin, tauraron dan adam din yana da inganci sosai, ta yadda zai iya gudanar da ayyukan binciken yanayi, a sararin sama ko cikin gajimarai, a sararin samaniyar kasar Sin da kewayenta, ta yadda za ta iya ba da cikakkun bayanai game da ainihin hasashen yanayi.
Sashen kula da hasashen yanayi na kasar Sin shi ne zai fi amfani da wannan sabon samfurin tauraron dan adam.
A lokuta baya dai, kasar Sin ta samu nasarar harba taurarin dan adam masu hasashen yanayi guda 14, kuma har ya zuwa yanzu, 7 daga cikinsu suna aiki a can sararin sama. (Ahamd Fagam)