in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta harba wani tauraron dan Adam da zai rika bibiyar yanayin iskar da ake shaka ta carbon dioxide
2016-12-22 11:23:20 cri

Kasar Sin ta harba wani tauraron dan Adam ta wani roka mai nisan zango, daga wata tashar kaddamar da tauraron dan Adam dake arewa maso yammacin kasar, da misalin karfe uku da minti Ashirin na safiyar yau Alhamis.

Baya ga Amurka da Jamus, Kasar Sin dai ita ce kasa ta uku da za ta yi amfanin da tauraronta na dan Adam waje bibiyar yanayin iskar.

Yin Zengshan da ya tsara tauraron ya ce, tauraron na Tansat mai nauyin kilogaram dari shida da ashirin da aka harba sararin samaniya da nisan kilomita dari bakwai, zai rika bibiyar yadda iskar da ake shaka ta carbon dioxide ke zagayawa da kuma yadda ake samar da ita .

Tauraron zai kuma taimaka wajen fahimtar sauyin yanayi tare da samar da ingantattun bayanai ga mahukunta a kasar Sin.

A aikin shekaru uku da zai yi, zai rika duba yanayin iskar a fadin duniya baki daya a ko wadannen kwanaki goma sha shida.

Baya ga wannan, yana kuma da wasu na'urori da za su rika duba yanayin dazuzzuka da ayyukan gona. (Fa'iza)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China