Tuni dai Man city ta tabbatar da hakan, tana mai cewa dan wasan mai shekaru 19 da haihuwa, zai taka mata leda ne har zuwa shekaru 5 masu zuwa, ko da yake ana sa ran bada aron sa ga kulaf din Girona dake Sifaniya, a shekarar sa ta farko karkashin kwantiragin.
Kafofin watsa labarai na kasar Brazil dai sun bayyana cewa, kungiyar ta Man City ta sayi dan wasan ne kan kudi har Euro miliyan 12, wanda hakan ke nuna cewa, shi ne dan wasa mafi tsada da kungiyar Vasco ta yi cinikin sa a tarihin ta.
Game da hakan, mahukuntan kulaf din na Vasco sun yiwa Douglas fatan alheri, suna masu burin ganin tauraruwar sa ta haskaka, a kwallon da zai fara bugawa a Turai.
Douglas shi ne dan wasa na 2 daga Brazil wanda ya koma Manchester City, kasa da shekara guda bayan da dan wasan gaban Palmeiras Gabriel Jesus ya tsallaka zuwa kungiyar a watan Janairun da ya gabata.
A nasa bangare, daraktan kungiyar Man City Txiki Begiristain, ya bayyana farin cikin sa da isowar Douglas, yana mai cewa dan wasan na da matukar hazaka, kuma sauran 'yan wasan kungiyar na fatan za su taka leda tare da shi domin daga darajar kulafi din. (Saminu Alhassan)