Vivian wadda ta lashe gasar tseren duniya ta gudun mita 10,000, ita da dan tseren kasar ta Kenya Geoffrey Kamworor, wanda shi ma ya taba lashe gasar rabin gudun yada kanin wani ta duniya, sun bayyyan cewa ba za su shiga gasar dake tafe cikin watan Maris ba.
Da take karin bayani game da hakan, Vivian ta ce ta na shirin shiga gasar Diamond League wadda za a gudanar a nahiyar Turai, domin share fagen tunkarar gasar Olymphic ta birnin Rio.
Ta ce duk wata gasa da za a gudanar a gida kafin gasar ta kasar Brazil, za ta zamo share fage ga babbar bukatar ta, wato lashe lambar zinari a gasar ta Olymphic. Kalaman 'yar tseren dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan da ta lashe gasar rundunar 'yan sandan kasar Kenya, wadda ita ce gasar tsere mafi girma da ake gudanarwa a kasar. Gasar da kuma mafi yawan wadanda suka yi nasara a cikin ta, ke samun damar wakiltar kasar a sauran gasannin kasa da kasa.
Bisa tarihin gasannin da ta halarta, Vivian ta lashe gasar nahiyar Afirka a shekarar 1998 a birnin Marrakech, na kasar Morocco, ta kuma lashe lambar zinari ta duniya ajin matasa a shekarar 2000.(Saminu Alhassan)