in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kulub din Kenya ya yiwa Rabat fintinkau a gasar tsere
2016-03-16 13:40:13 cri
Kungiyar wasanni ta kasar Kenyan tayi nasarar shatile kafar takwararta ta kasar Morocco Rabat a gasar gudun yada kanin wani, bayan da yayi nasarar cinye dukkan nin lambobin yabo a wasannin maza dana mata da aka fafata a Lahadin data gabata.

A bangaren 'yan wasa maza, Sammy Kigen ya samu lambar yabo ta zinare, bayan yayi nasara a wasan tseren a cikin kasa da sa'oi 2 da dakika 9, yayin da Alfred Kering yazo da 2:10:30 sai kuma Kipsang Kipkemoi dake bi musu baya da 2:11:59.

A bangaren mata kuwa, Pamela Rotich tayi nasara a karo na biyu a wasan gudun famfalakin, bayan gudun kasa sa'oi 2 da dakika 28, yayin Esther Chemtai da Naomy Tuei suke bi mata baya a gudun kasa da sa'oi 2 da dakika 28 d kuma sa'oi 2 da dakika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China