in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin NDB ya kaddamar da cibiyarsa ta nahiyar Arika a Johannesburg
2017-08-18 09:51:55 cri
Sabon bankin raya kasashen BRICS NDB, ya kaddamar da ofishinsa na yankin Afrika a Johannesburg, karkashin jagorancin shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma.

Jacob Zuma ya bayyana kaddamawar a matsayin abun da ya shiga tarihi, yana mai bayyana kudurin kasashen BRICS na raya nahiyar Afrika tare da samar da harkokin kasuwanci.

BRICS dai na nufin harufa na farko na kasashe mambobin kungiyar da suka hada da Brazil da Rasha da Indiya da China da kuma South Afrika wato Afrika ta Kudu.

Shugaba Zuma ya ce tuni bankin ya raba kashin farko na jerin rancen da zai bayar wanda ya kai dala biliyan 1.5, wanda ya bayyana a matsayin babban ci gaba, idan aka hada da sauran nasarori da bankin ya samu kamar ba da takardar lamuni ga kasuwannin hannayen jari na kasar Sin wanda kudinsu ya kai kimanin dala miliyan 450.

Ya ce suna sa ran bankin, ta hannun cibiyarsa ta Afrika, zai bada gudunmuwa wajen gaggauta zuba jarin a fannin samar da ababen more rayuwa da suka hada da makamashi da sufuri da ruwa da sauran bangarorin masu amfani, yana mai cewa suna da babban buri a kan ofishin.

Jacob Zuma ya kara da cewa, yayin da bankin ke bada dama ga samun mambobi, yana sa ran kasashen Afrika za su shiga sahun farko na masu son zama mambobinsa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China