Ministan ya fadi haka ne a yayin taron manema labarai da aka shirya a wannan rana dangane da taron shugabannin kasashen BRICS karo na tara da kuma taron shawarwari tsakanin kasashen da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa da kasashe masu tasowa dake tafe.
Ministan ya ce, tattalin arziki wani muhimmin bangare ne da ko da yaushe kasashen BRICS ke gudanar da hadin gwiwa a kai, wanda kuma ya kawo wa al'ummar kasashen moriya matuka. A yayin da hadin gwiwar kasashen ke kara fadada, bangaren siyasa ya zama wani muhimmin fanni a hadin gwiwar kasashen.
Ministan ya kara da cewa, a yayin da kasar Sin ta karbi jagorancin karba-karba na kungiyar a wannan shekara, kasarsa ta Sin za ta mai da hankali wajen ganin an aiwatar da hadin gwiwa a fannin cudanyar al'umma, baya ga fannonin tattalin arziki da siyasa, ta yadda cudanyar al'umma za ta kasance muhimmin bangare na uku na hadin gwiwar kasashen BRICS.
Baya ga haka, ministan ya bayyana cewa, daga yammacin ranar 3 ga zuwa safiyar ranar 4 ga watan Satumba, kasar Sin za ta shirya dandalin tattaunawa game da masana'antu da kasuwanci, na kasashen BRICS mafi girma a tarihi, taron da shugaba Xi Jinping zai halarta, ya kuma gabatar da jawabi. Daga bisani kuma, da safiyar ranar 4 ga watan, za a bude shawarwarin shugabannin kasashen BRICS, a cibiyar taron kasa da kasa dake Xia'men. A safiyar ranar 5 ga wata kuma, shugaba Xi zai shugabanci taron tattaunawa tsakanin kasashe masu samun saurin bunkasuwar tattalin arziki, da na masu tasowa.(Lubabatu)