in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin NDB ya kafa reshensa na farko a nahiyar Afirka
2017-08-18 19:23:04 cri
An kaddamar da reshen banki mai kula da harkokin nahiyar Afirka, na babban bankin raya kasa karkashin laimar kungiyar kasashen BRICS ko (NDB), a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu a jiya Alhamis, dangane da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying, ta gabatar da sakon taya murnar kafuwar wannan reshe na bankin a yau Jumma'a.

A cewarta, kasar Sin za ta yi kokarin sanya reshen bankin na NDB taka rawar gani, a fannin taimakawa jama'ar nahiyar Afirka wajen raya kasashensu.

Ta ce wannan reshen banki shi ne irinsa na farko da bankin NDB ya kafa. Ana kuma da niyyar mai da shi wata tagar bankin NDB, ga daukacin kasashen dake nahiyar Afirka. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China