in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen BRICS za su yi taro karo na 9 a Xiamen na kasar Sin
2017-08-30 10:25:30 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya sanar a yau Laraba cewa, za a gudanar da taron shugabannin kasashen BRICS wato Brazil, Rasha, Indiya, Sin da Afirka ta kudu daga ranar 3 zuwa 5 ga wata mai zuwa a birnin Xiamen dake lardin Fujian na kasar Sin. Babban taken taron shi ne kyautata huldar da ke tsakanin kasashen BRICS, a kokarin samun kyakkyawar makoma

A yayin taron, ana sa ran za a yi taron tattaunawa a tsakanin kasashe masu saurin bunkasar tattalin arziki da kasashe masu tasowa, bisa babban taken "zurfafa hadin gwiwa domin samun moriyar juna, da kara azama kan samun ci gaba tare."

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ne zai shugabanci taron shugabannin da taron tattaunawar, tare da halartar bikin bude taron tattaunawar kasashen BRICS ta fuskar masana'antu da kasuwanci da sauran harkoki. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China