Firaiministan Li Keqiang ya fada a yau Talata cewa, kasar Sin ta cimma gagarumar nasara fiye da yadda aka yi tsammani wajen bunkasa fannin masana'antu da fasahar kirkire kirkire.
Li ya fada a lokacin da yake gabatar da jawabi yayin bude taron kolin shekara na New Champions 2017 wanda aka fi sani da taron dandalin tattalin arziki na Davos, wanda ya gudana a birnin Dalian na kasar Sin.
Ya ce, an yiwa sabbin kamfanoni 14,000 rijista ko wace rana a cikin shekaru uku da suka gabata, kuma kashi 70 cikin 100 na kamfanonin sun fara aiki gadan gadan, ban da haka kuma a watan Mayun wannan shekara, adadin sabbin kamfanonin da aka yi musu rajista a ko wace rana ya kai 18,000, in ji mista Li.(Ahmad Fagam)