in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilan mambobin kasashen BRICS sun tattauna game da yin hadin gwiwa kan ta'ammali da kwayoyi
2017-08-17 10:33:08 cri
Wakilan mambobin kasashen BRICS sun cimma matsaya na samar da wani tsarin musayar bayanai da yin hadin gwiwa a tsakaninsu game da batun dakile ta'amali na haramtattun kwayoyi.

Sama da jami'an sashen hana ta'ammali da miyagun kwayoyi 20 ne daga kasashen Brazil, Rasha, India, Sin da Afrika ta kudu suka halarci taron, wanda aka gudanar a ranar Laraba a Weihai, wani birni na tashar ruwa a lardin Shandong na gabashin kasar Sin.

A lokacin taron, wakilan sun tattauna batutuwa da dama, ciki har da batun duba irin sinadaran da ake amfani da su wajen sarrafa kwayoyi, da bada horo ga jami'an dake aikin lura da kwayoyi, da kuma yin musayar kwarewa tsakanin kasashen.

Bangarorin sun kuma amince da ka'idojin gudanar da ayyukan yaki da ta'ammali da haramtattun kwayoyi na BRICS, wanda kuma ake sa ran gabatar da shi ga kwamitin shirya taron koli na BRICS karo na 9.

Kasar Sin wadda ta karbi shugabancin BRICS a wannan shekara, ita ce za ta karbi bakuncin taron koli na BRICS karo na 9 a birnin Xiamen, dake lardin Fujian a watan Satumbar bana. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China