in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Bankin NDB: Taron kungiyar BRICS a Xiamen zai kara karfafa dangantaka
2017-08-11 10:19:00 cri
Shugaban sabon bankin raya kasashe, NDB na BRICS K.V Kamath, ya ce taron kungiyar BRICS dake karatowa, zai taimakawa kasashe 5 mambobin kungiyar, gina huldar tattalin arziki mai karfi tsakanainsu, tare da samar da kyakkyawar makoma.

Da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, K.V Kamath ya ce, sama da shekaru 10 da suka gabata ne kasashen Brazil da Rasha da Indiya da China da Afrika ta kudu suka hadu tare da kafa kungiyar BRICS. Kuma sakamakon dinkewar tattalin arzikinsu ne ya samar da bankin NDB.

Yayayin taron kungiyar BRICS na kasashe masu samun ci gaba cikin sauri karo na 9, da zai gudana a birnin Xiamen na kasar Sin a farkon watan Satumba, K.V Kamath zai gabatar da nasarorin da bankin ya samu cikin sama da shekaru 2 tare da bayyana inda ya sa gaba a shekaru 2 zuwa 3 masu zuwa.

An bude bankin wanda kasashen BRICS suka kafa a shekarar 2014, a watan Yulin 2015 a birnin Shanghai, inda ya fara aiki a farkon shekarar 2016.

Shugaban Bankin ya kara da cewa, ci gaban da kasashen ke samu, musammam irin wanda ake gani a kasar Sin, ya bayyana karara irin muhimmanci da ke akwai na tabbatar da dorewarsa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China