Wannan roka ita ce gwajin roka ta biyu da ake shirin harbawa bisa aikin nazarin sabon nau'in roka na "Long March-5", kuma idan an samu nasarar harbar rokar lami lafiya, hakan zai shaida cewa, an kammala aikin kirkiro sabuwar rokar mai daukar kaya.
A wannan karo, bayan da aka harba rokar, za ta kai wani tauraron dan Adam mai taken Shijian-18 zuwa sararin samaniya. Wannan tauraron dan Adam din dai, ana shirin yin amfani da shi wajen tantance wasu fasahohi masu muhimmanci masu alaka da tauraron dan Adam, gami da wasu fasahohi masu ci gaba ta fuskar harkar sadarwa.
Rokar "Long March-5" ita ce roka mafi girma da kasar Sin ta kirkiro, wadda ta shaida fasahohi mafi ci gaba na kasar Sin a fannin samar da roka mai daukar kaya. An harba nau'in wannan roka ta farko ne a ranar 3 ga watan Nuwamban shekarar 2016, a filin harbar kumbuna na Wenchang dake lardin Hainan na kasar Sin.(Bello Wang)