in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin jakadancin Sin da ke Zambia ya shirya liyafa ga daliban da za su Sin karo ilimi
2017-08-28 10:41:49 cri

Jiya Lahadi ne, ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Zambia ya shirya liyafar ban kwana a birnin Lusaka, babban birnin kasar ga daliban da suka samu tallafin guraben karo ilimi a kasar Sin, tare da ba da dama ga daliban da suka koma gida bayan kammala karatu a kasar Sin wajen nuna fasahar wasanni. Inda dalibai 26 suka nuna fasahohin da suka koya a kasar Sin a fannonin wake-wake da raye-raye.

Rahotanni na cewa, a shekarar 2017 da muke ciki kasar Sin ta samar da tallafin guraben karo ilimi ga daliban kasar Zambia kimanin 150.

Jakadan kasar Sin da ke Zambia Yang Youming ya nuna cewa, ba da ilmi wani muhimmin fanni ne na mu'amalar da ke tsakanin Sin da Zambia, wanda ya samu saurin bunkasuwa karkashin inuwar tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC. Kasar Sin ta zama gida ga daliban Zambia dake neman karo ilmi, kuma kawo yanzu akwai dalibai fiye da 3500 da ke karatu a kasar Sin, kuma gwamnatin kasar Sin ta samar da kudin tallafin karatu zuwa ga daliban kasar kusan 800.(Kande)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China