in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Zambiya ya kafa dokar ta baci
2017-07-06 14:43:52 cri

A ranar Laraba shugaban kasar Zambiya Edgar Lungu ya kafa dokar ta baci a sakamakon tashin hankali da ya barke a kasar, lamarin da ke cigaba da haddasa hasarar dokiyoyin gwamnati.

Da yake yiwa jama'ar kasar bayani ta gidan talabijin, shugaban ya ce, tilas ne ta sanya suka dauki wannan mataki, domin suna burin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar, kana suna son al'ummar kasar su samu cikakken tsaron da ita kanta kasar, ya ce ba su da wani zabi da ya wuce daukar wannan matakin.

Lungu ya bayyana cewa ya yi amfani da sashe na 31 ne na kundin tsarin mulkin kasar wanda ya ba shi damar kafa dokar ta bacin da zarar aka samu yanayi irin wanda kasar ke fuskanta a halin yanzu. Ya kara da cewa, tuni aka aikewa majalisar dokokin kasar wannan batu domin neman amincewarta.

A makon jiya ne dai, 'yan sanda a kasar suka fitar da wasu bayanan sirri dake nuna cewa akwai wasu mutane dake shirin haddasa fitina domin lalata dukiyar gwamnati.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China