Edgar Lungu ya ce sake zaben Paul Kagame alama ce dake nuna yakinin da al'ummar Rwanda ke da shi a kan shugabanci da manufofinsa ga kasar.
Wata sanarwar da ofishin shugaban kasar ya fitar ta ce Zambia na sa ran ci gaba da hada hannu da gwamnatin Rwanda wajen magance batutuwa da suka shafi kasashen biyu da kuma sauran kasashe.
Paul Kagame mai shekaru 59 da ya lashe zaben shugaban kasar Rwanda da gagarumin rinjaye, ya samu wa'adi na 3 kan mulki, inda zai dora akan shekaru 17 da ya yi yana jan ragamar kasar.
A cewar sakamakon da hukumar zaben Rwanda ta fitar, shugaban ya lashe zaben ne da kashi 98.79 na kuri'un da aka kada, inda ya samu kuri'u miliyan 6.6. (Fa'iza Mustapha)