in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya zama wajibi Afirka ta magance matsalar ababen more rayuwa domin samar da cigaba in ji wani minista
2017-08-22 09:59:36 cri
Ministan kudin kasar Zambia Felix Mutati, ya yi kira ga kasashen Afirka, da su dauki matakan bunkasa samar da ababen more rayuwa, tare da hade sassan nahiyar wuri guda, ko a kai ga fadada ci gaban nahiyar yadda ya kamata.

Mr. Mutati ya yi wannan jan hankali ne yayin bikin bude wani taro na yini 2 na masu ruwa da tsaki wanda aka gudanar a birnin Johannesburg, yana mai cewa ya kamata kasashen nahiyar su hanzarta daukar wadannan matakai, domin kaucewa mummunan sakamako a nan gaba.

Ya ce Afirka ta gaza a fagen takara da sauran nahiyoyi, saboda karancin kayayyakin more rayuwar jama'a da take fama da shi. Kaza lika a cewar sa, akwai bukatar kashe kudi da yawan su ya kai dalar Amurka kusan biliyan 93 a duk shekara, a ayyukan rage gibin kayayyakin bukatar al'umma a nahiyar.

Mr. Mutati ya ce karin wasu hanyoyin da za a bi a nahiyar domin cimma wannan buri, sun hada da fadada dabarun samar da kudaden gudanar da ayyuka, da amfani da kayayyakin more rayuwa ta hanyoyi mafiya dacewa, da samar da fasahohi masu haifar da ci gaba.

Bugu da kari ya ja hankulan gwamnatocin nahiyar, da su rika baiwa sassa masu zaman kan su dama ta zuba jari, ko a kai ga cimma wannan buri.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China