Ana dai sa ran halartar wakilai kimanin 500, ciki hadda masu dakin shugabannin kasashen Malawi, da Mali da kuma Uganda, za kuma a nazarci hanyoyi da dabarun bunkasa ilimi tsakanin matasa, da inganta kwarewar su ta fuskar jagoranci, da cudanya tsakanin yankuna, da nahiyoyi, da ma mataki na kasa da kasa, musamman a fannin tattauna batutuwa ilimi da daidaiton jinsi. Daga karshe ana fatan hakan zai dace da manufar kungiyar AU game da ciyar da ilimi gaba, kamar yadda yake kunshe cikin ajandar ci gaban nahiyar ta 2063.
Wata sanarwa daga ofishin ministan ilimin kasar ta Zambia Dennis Wanchinga, ta bayyana taken taro na wannan karo da "yunkurin samar da daidaito a fannin ilimi a nahiyar Afirka". Cikin sanarwar Mr. Wanchinga ya bayyana tasirin wannan taro da zai gudana tsakanin ranekun 23 zuwa 25 ga watan nan da muke ciki, yana mai cewa dama ce ta duba dukkanin sassa na ciyar da ilimin mata da matasa gaba a nahiyar Afirka.(Saminu Alhassan)