in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin da Zambia za su kara zurfafa hadin gwiwa a fannin aikin gona
2017-08-04 09:20:38 cri
Kasashen Sin da Zambia sun bayyana anniyarsu ta kara zurfafa hadin gwiwa a fannin aikin gona, a wani mataki na tallafawa juna tare da karfafa dangantaka a wannan fanni.

Jakadan kasar Sin dake kasar Zambia Yang Youming shi ne ya sanar da hakan a jiya Alhamis, yayin da yake jawabi a bikin bude taron kolin hadin gwiwa da raya aikin gona tsakanin Sin da Afirka. Ya ce kasashen biyu sun yanke shawarar cin gajiyar wannan fanni ne, ganin yadda Allah ya horewa Zambia yanayin da ya dace da aikin noma, yayin da a hannu guda kuma kasar Sin take da jari, da fasahohi da kuma kwarewa a wannan fanni.

Jakada Yang ya ce, ya yi imanin cewa, idan har kasashen biyu suka hada karfi da karfe, hakika hadin gwiwar sassan biyu a wannan fanni zai haifar da kyakkyawan sakamako.

A nata jawabin ministar aikin gona ta kasar Zambia Dora Siliya, yabawa ta yi da irin taimakon raya kasa da kasar Sin ke baiwa kasarta. Ta ce, kasar Sin ta taimakawa kasarta a fannoni da dama, ciki har da fannin aikin gona da ake kokarin zamanintarwa a halin yanzu.

Ministar ta ce kasarta ta koyi fasahohin aikin gona da dama daga kasar Sin, yayin da kasar take kokarin fadada wannan fanni, wanda a baya ta dogara ga noman masara kadai.

Cibiyar hada fina-finai da shirye-shiryen talabijin game da aikin gona ta kasar Sin da kamfanin Global Max Media tare da hadin gwiwar majalisar 'yan kasuwa da aikin gona ta kasar Zambia ce suka shirya taron kolin. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China