in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu tsattsauran ra'ayi sun hallaka sojoji 5 a gabashin Libya
2017-07-31 11:18:45 cri
Kafafen yada labaran kasar Libya sun rawaito cewa, mayaka masu tsattsauran ra'ayi sun hallaka sojojin kasar 5 a gabashin kasar, kana sun jikkata wasu sojojin 4 a birnin Darna dake gabashin kasar.

An kashe sojojin 3 nan take a lokacin da 'yan bindigar suka afakawa sojojin a wajen binciken ababen hawa dake kudancin Darna, kamar yadda kamfanin dillancin labaran hukumar sojin kasar ya ruwaito.

'Yan ta'addan sun kuma harbo jirgin saman yakin sojojin a Darna a ranar Asabar, kamfanin dillancin labaran ya ce, harin ya hallaka matukin jirgin da soja guda, kana ya jikkata wani sojan guda. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China